Connect with us

Labarai

EFCC Ta Fara Yin Bincike Kan Tsohon Gwamnan CBN

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fara gudanar da bincike kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele a ranar Juma’a.

 

Hukumar na bincikar Emefiele akan bashin dala biliyan 15 da aka ciyo daga ƙasashen waje.

 

Sannan Emefiele zai kuma yiwa hukumar bayani akan yadda babban bankin ya kashe Naira biliyan 74.84, wajen samarwa da kuma fitar da kudade, ciki har da sabbin takardun kuɗi na Naira da sauran wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.

 

Zarge-zargen da hukumar ta ke yi masa kari ne akan zargin badakala, wanda jami’in bincike na musamman, Jim Obazee wanda ke duba ayyukan CBN ya bankado.

 

Obazee wanda kwamitinsa ke hada kai da hukumar binciken yan sandan Najeriya, ya kuma mika rahoton wucin gadi akan CBN ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

 

Ya ce ya zuwa yanzu kwamitin jami’in EFCC ya fara bincikar Emefiele kan zarge-zarge shida da ake yi masa.

 

 

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

ISWAP Sun Kai Hari Kan Jami’an Lafiya A Borno

Published

on

Wasu da ake kyauta zaton mayaƙan ƙungiyar Boko Haram tsagen ISWAP ne sun hallaka baturen ƴan sanda a wani hari da su ka kai jiya Litinin.

Maharan, sun hallaka baturen ƴan sandan ne a yayin da su ka kai hari kan wasu jami’an lafiya.

Ma’aikatan lafiyan sun kira don sanar da jami’an ƴan sanda dangane da harin da aka kai musu, sai dai jami’in ya rasa ransa yayin da ya ke ƙoƙarin daƙile harin su ka hallakashi

Rahotanni sun nuna cewar mayaƙan sun kai hari Marte, su ne da misalin ƙarfe 07:30pm na daren jiya.

Wasu bayanai daga majiya cikin jami’an tsaro, sun ce an kashe baturen y’an sandan sannan an raunata wasu mutane biyu.

Zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance dangane da kisan babban jami’in

Continue Reading

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Sama Da Mutane 20 A Abuja

Published

on

Wasu da ake kyauta zaton ƴan bindiga ne sun sun yi garkuwa da mutane 20 a wani sabon hari sa su ka kai Dawaki, kusa da Kubwa da ke Abuja.

Ƴan bindigan sun kai harin rukunin gidajen Frank Opara tare da yin awon gaba da mutane 20.

Shugaba a yankin Dawaki Tunde Abdurrahik wanda ya shaida hakan ga manema labarai, ya ce ƴan bindigan sun kai harin ne da ƙarfe 7:30 na daren Lahadi wayewar jiya Litinin.

Ya ce ƴan bindigan sun kusa su 50, ɗauke da makamai, sun ɓalle ƙofofin gidaje hida sannan su ka yi garkuwa da mutanen.

Yayin da take bayani dangane da harin, mai magana da yawun ƴan sanda a Abuja Josephine Adeh ta ce jami’ansu sun kai ɗaukin gaggawa wanda har ta kai ga sun yi musayar wuta da maharan.

Ta ce kwamishinan ƴan sanda da kansa ya jagoranci mayar da martani ga ƴan bindigan, kuma an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su yayin da ƴan bindigan su ka gudu ɗauke daa rauni harbi a jikinsu.

A ranar Lahadin dai, sai da ƴan bindiga su ka yi garkuwa da mutane Biyar a Shagari Quaters da ke Dei-Dei duka a Abuja.

Continue Reading

Labarai

An Samu Zaman Lafiya A Abuja Tun Bayan Da Tinubu Ya Zama Shugaban Ƙasa – DSS

Published

on

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce an samu ƙaruwar zaman lafiya da raguwar ta’addanci a cikin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da yake gab da cika shekara guda a kan karagar mulkin ƙasar, darakta a hukumar DSS Adamu Gwary ya ce an samu raguwar aikata laifuka a Abuja tun bayan hawan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, Adamu ya ce an samu ci gaba ta ɓangaren tsaro a Abuja tun bayan da aka naɗa Nyesom Wike a matsayin ministan Abuja a watan Agustan shekarar 2023 da ta gabata.

Wannan bayani nasa na zuwa ne ƙasa da kwana uku da aka kai mabambantan hare-hare aka sace mutane da dama a Abuja.

Daraktan ya ce a baya ana kiransu don sanar da su matsalar tsaro a kowacce rana, sai dai a yanzu ana iya shafe mako guda ba tare da an sanar da su wata matsala na faruwa ba.

La’akari da yadda aka samu ƙarancin rahoton kai hareharen, ya ce an samu cigaba a ɓangaren tsaron matuƙa a Abuja.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: