Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa ya zuwa yanzu Kotun daukaka kara ba ta bai’wa lauyoyinta ainihin kundin hukuncin kotun da ta kwace kujerar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ba.

Jam’iyyar ta ce jinkirin fitar da asalin takardun hukuncin na barazana ga kokarin jam’iyyar na dawo da kujerar gwamnan na Kano da kotu ta kwace masa.
Mukaddashin shugaban Jam’iyyar na kasa Abba Kawu Ali ne ya yi korafi a ranar Litinin.
Kawu ya ce rashin ba su kundin hukuncin da kotun ta yi na iya fara shiga kwanaki 14 da doka ta ware da za su iya daukaka kara a kotun Koli.

Jam’iyyar ta ce rashin bai’wa jam’iyyar takardun hukuncin ka iya jefa jam’iyyar da gwamnan Abba Kabir Yusuf da kuma lauyoyin jam’iyyar cikin damuwa, a lokacin da lauyoyin ke aikin daukaka kara domin samun adalci a gaban Kotun Koli.

Jam’iyyar ta NNPP na wannan korafin ne bayan da kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin kotun baya na kwace kujerar gwamnan na Kano.