Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun sace mutane 39 bayan sun kashe mutum huɗu a wasu yankunan Abuja da kuma Jihar Neja.

A ranar Juma’a ’yan bindiga suka kutsa yankin Azu a Jihar Neja, suka kashe mutane uku suka sace wasu takwas.
Kafin nan a ranar Alhamis ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kuduru, Karamar Hukumar Bwari a Birnin Tarayya, suka yi garkuwa da mutane 18.

Da farko a ranar Asabar, 23 ga Disamba, ’yan bindiga a Jihar Neja sun mamaye yankin Garam da ke makwabtaka da Bwari, suka kashe wani faston Cocin Redeemed (RCCG), suka yi garkuwa da wasu mutane 13.

Wata ’yar yankin Garam, Misis Juliana, ta ce a gidan farko da ’yan bindigar suka yi kuskuren shiga suka tambayi gidan faston.
Ta ce yan bindiga sun shiga wani gida, suka tisa keyar wasu yara maza biyu domin su kai su gidan faston.
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kuma shiga gidan wani soja, suka nemi matarsa ta ba su bindigarsa da kakinsa.