Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana damuwa kan matsalar rashin biyan kudaden aikin hajjin bana.

Akwai alamun cewa yawan kujerun da aka ware wa hukumar na dubu 95 ba za ta iya cike su ba a shekarar 2024.

Hukumar ta sanya 31 ga watan Disamba a matsayin ranar karshe na biyan kudaden a sassan hukumar ta jihohi.

Har ila yau, hukumar ta sanya ranar ne don tabbatar da cewa ta samu yawan mutanen da za su sauke farali a wannan shekara.

Sannan tsarin zai taimaka wa hukumar wurin ganin ta fara shirye-shirye da hukumomin jigilar maniyya a Najeriya da kasar Saudiyya.

Sai dai tsadar kujerar da kuma sanya ranar rufe karbar kudaden ya sa yawan mutanen ya ragu sosoi fiye da yadda ake tsammani.

Duk da cewa hukumar ba ta sanar da cewa za ta kara wa’adin ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maniyyata ba su wuce dubu 25 ba ne suka biya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: