Shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano sun maka gwamnatin jihar a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja kan yunkurin gina gadoji biyu.

Shugabannin sun kai ƙarar gwamnatin Abba Kabir Yusuf gaban kotun saboda yunkurin gina gadojin sama biyu a Tal’udu da Ɗan’agundi duk da kuɗin kananan hukumomin.
Sun buƙaci kotun ta bada umarnin hana gwamnatin Abba amfani da kuɗaɗensu na asusun haɗin guiwa wajen gina gadojin saman guda biyu a cikin kwaryar birni.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin sun shigar da wannan ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1733/2023 ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba, 2023.

Wadanda suka shigar da karar su ne kananan hukumomi 44 da kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON), reshen jihar Kano.
Sai kuma waɗanda ake ƙara sune gwamnatin jihar Kano karkashin ,Gwamna Abba Kabir da kwamishinan shari’a kuma Antoni-Janar na jiha da Akanta na Kano.
Da yammacin jiya Juma’a, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ɗora harsashin fara ginin manyan gadojin guda biyu.
A jawabinsa, Abba Gida-Gida ya ce bisa al’adar gwamnonin da suka gabace shi, za a samar da kuɗin waɗannan manyan ayyuka ne daga asusun haɗin guiwa na jiha da kananan hukumomi.