Fitacciyar malamar addinin musulmi a Najeriya Malama Fatima Tasallah Nabilisi Bako MFR ta ja hankalin al’umma akan muhimmanci rake alkawari.

Malamar ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi a gurin bikin cikar Matashiya TV shekaru Bakwai da kafuwa.


Malama ta Sallah ta kara da cewa rike alkawari na da matukar muhimmacin a cikin rayuwar dan adam.
Sannan ta kara da cewa rukon al’kawari na kara kusanta mutum ga Allah a cikin dukkan al’amuransa na rayuwa.
