Wasu ɗalibai guda biyu sun rasa ransu a yayin da su ka shiga dam din Danbatta a Kano.



Hukumar kashe gobara a Kano ta tabbatar da mutuwar ɗaliban biyu wanɗanda dukkansu ƴan kasa da shekara 25 ne.
Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ya ce sun samu kiran waya ne daga wani Kwamared Ibrahim Umar Muhammad wand aya sanar da su cewar ɗaliban uku sun shiga dam ɗin Thomas kuma sun kasa fitowa.
Bayan samar da su jami’an hukumar da ke karamar hukumar Dambatta haɗin gwiwa da masunta su ka yi kokarin ceto mutum guda.
Yayin da biyun aka cetosu da yamma kuma a mace.
Daliban na karatun a kwalejin noma da kiwo da ke Danbatta, kuma tuni aka kai guda dake rage asibiti domin kula da lafiyarsa.
Lamarin ya faru a jiya Talata kamar yadda hukumar ta sanar.
Zuwa yanzu hukumar ta ce ta na ci gaba da bincike domin gano dalilin mutuwar tasu.