Ƙungiyar gwamnonin Najeriya, ta tabbatar wa ƙungiyar kwadago ta NLC da TUC cewa za ta goyi bayan karin albashin da zai ishi ma’aikata su yi rayuwa mai inganci

 

Jaridar Vanguard ta ruwaito gwamonin sun kuma bayyana cewa suna duba batutuwan da suka shafi alawus-alawus na jami’an shari’a da ababen more rayuwa na kotuna.

 

A farkon shekarar nan ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin bangarori uku da suka hada da wakilan gwamnati, ’yan kwadago, da ‘yan kasuwa.

 

Aikin kwamitin shi ne tantance mafi karancin albashi na Naira 30,000 da aka aiwatar a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da nufin kara kudin su fi haka.

 

Amma a baya-bayan nan, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun gabatar da bukatar biyan mafi karancin albashi na N615,000 ga kwamitin.

 

A kan wannan, kungiyar ta NGF, ta hannun shugabanta kuma gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ta fitar da sanarwa a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

 

Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa kwamitin mai wakilai 37 da aka dorawa alhakin duba mafi karancin albashin ma’aikata na kasa har yanzu bai kammala aikinsa ba.

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: