Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa EFCC ta ce har yanzu t ana aikin gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle.



Wata ƙungiya ce ta yi kira ga hukumar da ta ci gaba da binciken tsohon gwamnan na Zamfara don ci gaba da bincike a kan zargin sa ake yi a kansa.
Ana zargin tsohon gwamnan da yin sama da faɗi da zunzurutun kudi naira biliyan 70 yayin da yake jagorantar jihar tsakanin shekarar 2019 zuwa shekarar 2023.
Mai riƙon daraktan hulɗar da jama’a Wilson Uwajuren shi ya bayyana haka yayin da ƙungiyar APC aƙida su ka yi zanga-zanga don ganin an ci gaba da binciken tsohon gwamnan.
Ya ce a duk lokacin da su ka fara bincike a korafi ba sa dainawa a don haka ya tabbatar musu da cewar za a ci gaba da gudanar da bincike a kai.
Yayin da yake gabatar da takardar korafin, shugaban ƙungiyar APC Akida Musa Mahmud ya buƙaci hukumaar da ta sake buɗe sabon bincike a ka tsohon gwamnan dangane da rashawa a mulkinsa