Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kama wasu ‘yan siyasa da suka ba da gudummuwar kudade a yayin zanga-zangar da aka gudanar a fadin Kasar a cikin watan da muke ciki.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan a Jiya Talata a yayin taron majalisar tsofaffin shugabannin Kasar da aka gudanar a Abuja.
A yayin Taro Malam Nuhu Ribadu ya gabatar da rahoto mai taken “yadda zanga-zanga ta taba tsaron ƙasar”.

Taron na tsofaffin shugabannin kasar ya samu halarci tsofaffin shugabannin kasar Muhammadu Buhari da Goodluck Ebele Jonathan.

Yayin da kuma wasu daga cikin sauran shugabannin suka halarta ta shafin yanar zigo.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan siyasar da aka kama su na daga cikin manyan masu ɗaukar nauyin zanga-zangar da aka gudanar a Kasar.
Majiyoyin ta ce an kama mutanen ne a babban birnin tarayya Abuja,da Kano, Kaduna da Katsina duk da ke Arewacin Kasar.
Rubado ya ce sun gano wasu ’yan siyasa sun bayar da Naira biliyan 4 domin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin Kasar.
Kazalika ya ce gwamnatin Tinubu ta kuma ƙwace Naira biliyan 84 da aka turo daga ƙasashen waje domin rura wutar zanga-zangar a Kasar.