Rundunar yan sandan jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wasu mutane huɗu bayan da wuta ta konesu.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da haka wanda ya ce mutane hudun mala’ikan wani otel ne.

Ya ce lamarin ya faru a safiyar jiya Lahadi yayin da wuta ta kama wani bangare na mashaya da kuma otel din.

Da samun rahoton da su ka yi ne kuma su ka yi gaggawar kai ɗauki wajen.

Ya ce wutar ta kone mutane hudun da ba a kai ga ganosu ba.

Sannan a binciken da su ka yi sun gano biyu sun mutu ne bayan da su ka samu rauni a jikinsu

Ya ce lamarin ya faru a yankin Ejigbo a jihar ranar Asabar.

Sannan gawawaki huɗu da su ka kone an kai su asibiti.

Haka kuma wadanda su ka jikkata su ma an kaisu asibitin Isolo a nan ne aka tabbatar da mutuwar biyu daga ciki.

Yayin da guda daga ciki ke karbar kulawa daga likitoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: