Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya TCN ya ce a halin yanzu ya na aiki tukuru don tabbatar da an gyara wutar da ta samu matsala.

An samu katsewar daga babbar tashar wutar wanda hakan ya jefa miliyoyin yan Najeriya cikin duhu.
Katsewar ta kasance sau biyu cikin awanni 24.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce a wassu wuraren ma tuni an kammala gyaran kuma an kunna musu wutar daga ciki akwai Abuja.

Haka kuma kamfanin y ce zai ci gaba da bincike don gano dalilin katsewar wutar daga babbar tashar.
Tuni dai wasu daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki a jihohin Enugu, Kano, Kaduna su ka baiwa abokan cinikinsu hakuri bisa katsewar wutar da aka samu.