Sabon shugaban hukumar da’ar ma’aikata ta Kasa Abdullahi Bello ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin dawo da darajar aikin gwamnati a fadin kasar.

Bello ya bayyana hakan ne bayan da shugaban Kasa Bola Tinubu ya rantsar da shi a jiya Laraba a yayin taron Majalisar zartarwa ta Kasa a Abuja.
Sabon shugaban hukumar ya ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya dakile cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnatin kasar.

Bello ya kara da cewa gwamnatin kasar za ta iya kawo karshen dabi’ar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikata matukar aka samar da ingantattun tsare-tsare a Kasar.

Bello ya ce Najeriya na da shirye-shiryen da za su yaki rashawa kuma za a yi amfani da su wajen cimma muradin raba ma’aikata da cin hanci.