Akalla shaguna 103 ne suka kone a yayin tashin wata gobara a bangarem kayan abinci na babbar Kasuwar Gusau da ke Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi,inda rahotannin suka danganta tashin gobarar da wutar lamtarki, bayan sa’o’i kadan da dawowa da wutar.

Acewar Rahotannin gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren jiya Lahadin, inda kuma ta ci gaba da yaduwa, kafin jami’an hukumar kashe gobara na Jihar dana tarayya su kashe ta da misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwar kayan abinci Alhaji Inusa Saminu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Shugaban ya ce shagunan sun kone kurmus, a yayin tashin gobarar, inda ya ce ba za su iya kididdige yawan asarar da suka tafka ba a halin yanzu, wadda ta kai ta miliyoyim nairori.

Alhaji Saminu ya bayyana cewa daga cikin shagunan da wutar ta kone akwai manyan kantuna da ke dauke da busassu kayayyaki a ciki.

 

Bugu da kari Alhaji Saminu ya danganta barnar da gobarar ta yi da samun tsaikon zuwan jami’an hukumar kashe gobara gurin.

Acewarsa bayan kiran ofishin hukumar ta kashe gobarar da ke kusa, sun shaida musu cewa mota daya da suke da ita ta lalace tsawon lokaci.

Shugaban ya roki gwamnatin Jihar da ta samar da motocin kashe gobara da kayan aiki, inda ya ce wannan gobara ita ce ta shida da aka samu a kasuwanni a jihar, kuma hakan ya haifar da babbar asara a Kasuwannin, inda ya nemi da gwamnatin ta tallafawa wadanda gobarar ta shafa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: