Bayan tattaunawa mai zurfi, kungiyar ma’aikatan jami’o’in ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take yi, kamar yadda jaridar PUNCH ta tabbatar.

An dauki matakin ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa a hedikwatar kungiyar da ke Jami’ar Abuja a safiyar yau Litinin.
ASUU ta sanar da fara yajin aikin ne a ranar Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022, a Jami’ar Legas.
A halin da ake ciki, kakakin ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong, a wata hira da ya yi da jaridar PUNCH, ya bayyana cewa gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace don kawo karshen yajin aikin.
Ya ce, game da mataki na gaba, gwamnati ta riga ta kaddamar da kwamitin daidaita tsarin IPPIS, UTAS, da UP3.

Kuma hakan zai tabbatar da cewa gwamnati za ta biya tare da tsarin biyan kuɗi ɗaya kawai wanda zai daidaita duk abubuwan fasaha.

Ya ce, ba dalili ba ne yajin aikin ya ci gaba ganin yadda gwamnati ta himmatu wajen biyan mafi yawan bukatun kungiyar.