Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya wa’adin makonni 6, da kowa ya mayar da kudinsa cikin asusun ajiyar banki.

Ana saran gabatar da sabbin tsare-tsare nan da makonni shida domin sauya fasalin takardun kudi a fadin kasar.

A jiya ne dai babban bankin Nijeriya CBN ya fitar da sanarwar sauya fasalin takardun kudi.

Bankin ya sanar da cewar zai sauya fasalin takardun kuɗi daga naira 200 zuwa naira 1,000.

Sai dai wasu a ƙasar na kallon hakan a matsayin koma baya ga tattalin arziƙi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: