Sarkin ƙasar Swaziland King Msawati lll ya tabbatar da dokar cewa duk wani namiji a ƙasar wajibi ne ya auri mata 4. Ko ya tafi gidan yari.
Sarkin ya bayyana cewa a watan June dokar zata fara aiki, kuma gwamnati ta shirya tsaf wajen ɗaukar dukkanin nauyin komai na auren tare da gidajen da mazajen zasu zauna.
Wannan dokar da sarki Mswati lll ya tabbatar ya biyo bayan yawaitar Mata da ake fama dashi a garin tare da ƙarancin mazaje don haka gwamnati ta ɗauki wannan gabarar tabbatar da wannan doka.

A cewar sarki bijirewa dokar a tsakanin namiji ko mace ka iya jawo musu ɗaurin rai da rai.
Sarkin ya ƙara da cewa shi kanshi a halin yanzu yana da mata 15, da ƴaƴa 25.
Haka zalika mahaifinsa yana da 70 tare da ƴaƴa 150. A sabo da haka bai ga dalilin da wani zai bijirewa wannan doka ba.

