Babban bankin Najeriya ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa bankin ya baiwa bankunan ‘yan kasuwa umarnin ci gaba da karbar tsofaffin kudade da bankin ya dakatar.

Daraktan sanarwa na bankin Osita Nwanisabi ne ya bayyana hakan ta cikin wani jawabi da yayi a shafin Twitter na bankin.

Osita ya bayyana cewa labarin da ake yadawa cewa bankin yayi umarnin bankunan ‘yan kasuwa su ci gaba da karbar tsofaffin kudaden bashi da tushe balle makama.
Daraktan ya ce mutane su yi watsi da jita-jitar da babban bankin na CBN ne ya fitar da shi ba.

Nwanisabi ya kara da cewa daga cikin kdaden da aka sauyawa fasali naira 200 ce kadai za a ci gaba da karbar tsawon kwanaki 60.Babban bankin Najeriya ya karya rahotannin da ake yadawa cewa bankin ya baiwa bankunan ‘yan kasuwa umarnin ci gaba da karbar tsofaffin kudade da bankin ya dakatar.

Daraktan sanarwa na bankin Osita Nwanisabi ne ya bayyana hakan ta cikin wani jawabi da yayi a shafin Twitter na bankin.

Osita ya bayyana cewa labarin da ake yadawa cewa bankin yayi umarnin bankunan ‘yan kasuwa su ci gaba da karbar tsofaffin kudaden bashi da tushe balle makama.
Daraktan ya ce mutane su yi watsi da jita-jitar da babban bankin na CBN ne ya fitar da shi ba.

Nwanisabi ya kara da cewa daga cikin kdaden da aka sauyawa fasali naira 200 ce kadai za a ci gaba da karbar tsawon kwanaki 60.

Kafin Musanta jita-jutar sai da Osita Ya tabbatawa da BBC cewa bakunan ‘yan kasuwa za su ci gaba da karbar tsofaffin kudade,daga baya kuma bankin ya fitar da sanarwar musanta rahotan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: