Akalla mutane 80 ne aka bayyana suka mutu. Tare da jikkata da dama a wani hari da aka kai sansanin Yan ci rani, dake kasar libya.

An kai harin ne ta jirgin sama inda aka dinga sakin bama bamai a cikin sansanin yan ci rani dake Tripoli babban birnin kasar.
mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta kasar mai suna Usama Ali ya fada wa manema labarai cewa akalla mutane 120 ne yan ci rani suke cikin mawuyacin hali, wanda ake basu kulawar da ya dace.
Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ana cigaba da kai hare haren sansanin yan ci rani ta sama, inda Usama yace akwai yuwuwar adadin mutanen da suka hallaka ya karu ko wane lokaci daga yanzu.

