Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ‘yar takarar gwamna ta jam’iyyar APC Aishatu Ɗahiru Ahmad Binani ta shigar gabanta ta na mai kalubalantar zaben gwamnan Jihar Adamawa.

 

Kotun ta yi watsi da karar ne a yayin zaman da ta gudanar a ranar Juma’a.

 

Bayan shigar da karar da Binani ta yi, ta roki Kotun da ta dakatar da hukumar zabe ta INEC akan yunkurin da take na gurfanar da dakataccen kwamishinan zaben Jihar Hudu Yunusa Ari a gaban kotu, bayan da ya ayyanata a matsayin wanda ta lashe zaben Jihar.

 

Aishatu Binani ta roki kotun da ta dakatar da INEC din ne akan daukar mataki kan Hudu Ari har sai lokacin da za a yanke hukuncin karshe kan karar da ta shigar gaban kotun.

 

Binani ta kara da cewa gurfanar da Ari a gaban babbar Kotun zai kawo mata cikas a shari’ar da ta shigar gaban Kotun zabe saboda Ari ne babbar shaidarta a kotun.

 

Da take yanke hukunci mai shari’a Donatus Okorowo, ta ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar da Binani ta shigar.

 

Mai shari’ar ta bayyana cewa wadanda ake karar sun yi nasara, kuma zasu iya gurfanar da dakataccen kwamishinan zaben Jihar Hudu Ari.

 

Idan za a iya tunawa bayan Hudu Ari ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Jihar ta Adamawa, hukumar INEC ta kasa ta dakatar da shi daga bakin aiki, tare da bayar da umarnin a hukuntashi.

 

Inda kuma hukumar ta INEC ta ayyana Ahmad Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: