Gwamnatin Jihar Kano ta ce a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka a fadin Kasar ciki harda Jihar, wasu batagari sun dauke takardun shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje, da mai dakinsa Hafsat Umar, da kuma dansa Umar Abdullahi da karin wasu mutane Biyar akan zarge-zangen da ake yi masu na almundahar kudaden Jihar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jindadinsa dangane da lamarin a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido da ya kai kotun da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako a Jihar don ganin yadda batagarin suka yi barna.

Gwamna Abba ya ce abin kunya ne da Allah-wadai ganin yadda wasu makiyan Jihar, suka dauko hayar ɓatagari domin lalata daya daga cikin gine-ginen al’ummar Jihar masu cike da dumbin tarihi da nufin daƙile zargin da ake yiwa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da iyalansa da kuma hadimansa.

Sanarwar ta tabbatar da cewa ɓatagarin sun kuma lalata kusan dukkanin sassan babbar Kotun Jihar, ciki harda ofishin Alkalin Alkalai na Jihar, inda hakan ya haifar da asarar sama da Naira biliyan daya ta hanyar satar kayan ofishin da kuma lalata ofisoshin da kona motoci da sauran abubuwan amfani.
Gwamnan Abba ya ce barnar da batagarin suka yi shiryayyen abu ne da aka shirya shi da wata manufa mara kyau, domin sace takardun tuhume-tuhumen da ake yiwa Ganduje kan cin hanci da rashawa.
A yayin ziyarar gwamnan Abba ya kuma bayar da umarnin fara gyaran kotun nan take tare da kara jami’an tsaro a kotun, inda kuma ya mika sakon jajensa ga babbar Alkaliyar Jihar Dije Aboki tare da manyan alƙalan kotun faruwar lamarin.
Gwamnan Abba Kabir ya kuma ja kunnen matasan Jihar da su daina yadda ana amfani da su wajen tayar da tarzoma, inda ya bukacesu da su mayar da hankali wajen neman sana’o’in hannu domin samarwa da kansu kyakkyawar rayuwa da makoma tagari.
Acewarsa gwamnatin ba za ta gaza ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar.
Sannan gwamna Abba ya kuma yabawa al’ummar jihar bisa yadda suka bai’wa gwamnatinsa goyon baya da hadin kai, tare da addu’ar nemna Allah ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasar tattalin arziki a fadin Jihar.
A yayin ziyarar gwamnan Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Haruna Isah Dederi da Babban Magatakardar Kotun Alhaji Abdullahi Ado Bayero da kuma sauran alkalan babbar kotun ne suka yiwa gwamnan rakiya zuwa guraren da aka barnata.