ɗShugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya ce har yanzu farashin man fetur bai wuce kashi 55 kan yadda ake siyarwa a ƙasashen maƙofta ba.

Dangote ya bayyana haka a wata ziyara da hukumar ECOWAS ta kai masa a matatarsa.

A cewarsa a ƙasashen maƙofta ana siyar da litar mai mafi ƙaranci dala ɗaya daidai da naira 1,600.

A Najeriya kuwa su na sigar da mai naira 815 zuwa 820 kowacce lita.

Ya ce har yanzu yan Najeriya ba su san cewar kaso 55 kacal su ke biya a kan farashin man da ake siyarwa a ƙasashen maƙofta ba.

A cewar Dangote akwai wani albishir da zai a nan gaba, amma yana da kyau mutane su sani cewar matatar mai da ya samar ya yi ne domin yan Najeriya.

Ya ce ragin farashin da ake samu ana samu ne sakamakon matatun mai masu zaman kansu da ake da su a Najeriya.

Dangote ya ce al’ummar Najeriya za su ji daɗi ba da jimawa ba a sanadin matatar mai da ya samar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: