Akalla mutane 10 ne suka mutu yayin da mutane sama da 20 suka jikkata yayin da wani gida hawa biyu ya rushe a yammacin indiya.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar ta tabbatar da cewa, cikin mutanen da benen ya fadowa akwai wasu yara da basu kai shekaru 10 a duniya ba.

Daraktan hukumar Satyan Narayan Pradhan ya bayyana a shafinsa na twitter cewar, har yanzu suna ƙoƙarin ceto sauran mutane 25 waɗanda suka jikkata a sakamakon lamarin.

Sai dai an gaza gano sababin rushewar ginin, amma a kan samu makamancin haka a cikin watan yuni zuwa satumba sakamakon yawan ruwan sama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: