
sakamakon matsalolin cikin gidan da suka addabe su.
Ƙungiyar ta sanar da haka ne yayin gabatar da rahotan ta na wannan shekara.
Rahotan ƙungiyar na bana yace ƙasar Amurka da manyan ƙasashen Turai da suka mayar da hakkin Bil Adama a matsayin daya daga cikin manufofin su a ƙasashen waje tun lokacin yakin cacar baka, a yau sun kauda hankali daga kai.
Daraktan ƙungiyar Kenneth Roth, yace matakin ƙalubalantar take hakkin Bil Adama na raguwa, inda yake komawa kan ƙungiyoyin cikin gida.
Roth yace shugaba Donald Trump na Amurka ya mayar da hankali wajen rungumar shugabannin dake kama karya, rikicin ficewa daga kungiyar kasashen Turai ya mamaye Birtaniya, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron yana kalamai masu daɗi amma kuma baya iya aiwatar da su.
Daraktan yace ita ma Angela Merkel wadda tayi fice wajen yaƙi da matsalar, yaƙi da masu tsatsauran ra’ayin cikin gida ya ɗauke mata hankali.
Rahotan ya yabawa ƙasashe 57 dake ƙungiyar ƙasashen Musulmi ta IOC da suka tashi tsaye domin kalubalantar yadda ake cin zarafin yan kabilar Rohingya a Myanmar, duk da yake kasashen basu ce komai ba kan yadda China ke cin zarafin Musulmi ‘yan kabilar Uighur., dake chana.

