wata rana wani mai mashin yayi dare sai ya hadu da yan sanda suka tare shi, ko me yasa yayi dare, sai yace wallahi aiki ne yamai yawau shi yasa yakai dare, dan sanda yace to mun kamaka.
mai mashin yayita bada hakuri, can dan sanda yace to ya kawo 1000 daya sai ya tafi, mai mashin yace ga 500 dai, dan sanda yace wallahi bazai karba ba sai 1000, mai mashin yaga lokacin zai kure masa, sai ya mikawa dan sanda 1000 yace gashi yallabai shikenan ba kare bin damo, sai dan sanda yace zo nan, waye karan waye damon, mai mashin yace yallabai duk ni ne, sai dan sanda yace to jeka.


