Hukumar Hizbah a jihar Kano ta maganatu kan batun ƙulla auratayya da wani saurayi da budurwa suka yi a kafar sadarwa ta Facebook.
Daraktan hukumar Mallam Abba Sa id Sufi ya ce hakan karya dokar Allah ne kuma ba za su bari lamarin ya sha ruwa ba.
Ya ce wasa da addini ne yin hakan kuma aikin hukumar ne ladaftar da duk wanda yake yiwa addini karan tsaye.