Babban muhimmin aiki da ke gaban ministoci a hali, Yanzu da ake son su aiwatar shine fitar da yan Najeriya daga kangin Talauci, da tabbatar da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu sai uwa uba bunkasa tattalin arzikin kasa.

Jam’iyar ta bayyana hakan ne ta cikin wani sakon taya murna da ta aikewa Ministocin, wacce Sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya sanyawa hannu,inda jami’ar APC ta bukaci sabbin Ministocin da su nutsu sosai su kuma gudanar da ayyukansu yanda ya kamata.
Sanarwar ta kara da cewa, sabbin Ministocin da su tabbatar da nuna hali na gari bisa amincewar da Shugaban kasa tare da sauran yan Nijeriya suka yi musu ta hanyar zabar su don gudanar da ayyukansu a cikin hanzari domin tallafawa nasarorin da aka samu a sassa daban-daban Najeriya.

