Dan wasan kungiyar Liverpool kuma dan kasar Senegal, Sadio Mane, ya zama gwarzon dan kwallon nahiyar Afrika na shekarar 2019 a taron bikin da aka shirya ranar Talata, 7 ga watan Junairu, a kasar Masar.

Dan shekara 27 yayi takara da abokin wasansa a Liverpool, Mohamed Salah da dan kwallon Manchester City, Riyad Mahrez.
Ga jerin gwarazan:

Gwarzon dan kwallon Afrikan shekara Sadio Mane (Senegal da Liverpool)

Gwarzuwar ‘yar kwallon Afrikan shekara Asisat Oshoala (Nigeria & Barcelona)
Matashin dan kwallon shekara Achraf Hakimi (Morocco & Borussia Dortmund)
Kocin Afrikan shekara (Maza) Djamel Belmadi (Algeria)
Kocin Afrikan shekara (Mata) Desiree Ellis (South Africa)
Gwarzuwar kasa, shekarar 2019 Algeria Dan kwallon da yaci kwallo mafi kyau a shekara Riyad Mahrez
‘Yan kwallo 11 mafi kyau a Afrika
Andrey Onana,
Achraf Hakimi,
Kalidou Koulibaly,
Joel Matip,
Serge Aurier,
Riyad Mahrez,
Idrissa Gueye,
Hakim Ziyech,
Mohamed Salah,
Sadio Mane,
Pierre Emerick-Aubameyang
Muryar Yanci/matashiya