Rahotanni daga kasar Amurka ta bakin,

Hukumomin birnin Washington DC dake Amurka sun rawaito cewa , wani dan Najeriya da ya ziyarci kasar ya kamu da cutar Coronavirus kamar yadda gwajin da aka yi masa a wani asibiti da ke Maryland ya nuna.
Rfi hausa sun rawaito cewa Mai rike da kujerar Magajin Garin birnin , Muriel Bowser ta ce mutumin ya dauki lokaci a birnin Washington bayan ziyarar da ya kai daga Najeriya inda yake zaune da yan uwansa.

Jami’ar ta ce, sun tabbatar da kamuwar mutane biyu a birnin Washington, wato dan Najeriyar da kuma wani mazaunin birnin.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce, babu alamar cewa, dan najeriyan ya kamu da kwayar cutar ne tun a Najeriya.