Tun bayan Bullar Cutar corona virus ta raunana tattalin arzikin kasahen duniya ciki har da Najeriya.
Wannan dalili yasa farashin ‘danyen man fetur ke ta sauka kasa irin yadda bai taba kasancewa ba a tarihi .

A yanzu kowace gangar ‘danyen mai ana siyar dashi akan dalar amurka 11 ($11) wanda a hakan ma Najeriya bata iya siyar da man duk da wasu saukin da akai wa masu siya.
Kasashen da suka dogara da ‘danyen mai a matsayin babban hanyar shigar su a halin yanzu suna cikin tsaka mai wuya.
Najeriya ta na daya daga cikin kasashen da suke dagaro da man fetur sosai a matsayin kudin tafiyar da harkokin kasar.

Masana da masu ruwa da tsaki a harkar sun bayyana cewa yanzu akwai miliyoyin gangar mai a ajiye wanda ake jiran masu siya, Najeriya na fusakantar kalubalen karyewar farashin mai da kuma na masu siyan albarkatun man a kasuwannin duniya. Gashi kasar bata yi wani shiri na musamman ba domin adana ‘danyen albarkatun man ba .

Muryar yanci ta Rawaito cewa Wannnan kalubalen na karyewar darajar mai a kasuwannin duniya ba karamar barazana bace ga kasashe masu tasowa da kuma kasashen da mai ne babban hanyar samun kudaden shigar su .