Hukumar da ke kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cutar Corona za ta haifar da karuwar samun juna biyu da ba a yi shiri ba.

Hukumar ta yi hasashen cewa idan har aka yi wata shida cikin dokar hana fita, kusan mata miliyan 47 a kasashe masu karamin karfi ba za su samu kai wa ga hanyoyin da suka saba ba na matakan hana daukar ciki.
Hukumar ta ce za a iya samun juna biyu sama da miliyan bakwai saboda kulle da al’ummar duniya suke ciki.

Ta kuma yi gargadi kan karuwar rikici tsakanin ma’aurata da za a iya samu sama da milian 30 a tsawon wannan lokaci.
