Mahaifiya ga dan takarar majalissar dattijai a jamiyar APC A.A.Zaura ta shaki iskar yanci a Talata .

A.A.Zaura ya bayyana haka ne a shaifin sa na Facebook inda ya ce yana godewa Allah bisa nasarar ceto mahaifiya sa daga hannun masu garkuwa da suka sace ta.
Ya cigaba da cewa ina matukar godewa jami’an yan sanda da ma na farin kaya bisa kokarin da akai waje kubutar da mahaifiyar sa da gurin masu garkuwa.

Shima a bangaren sa jigo a tafiyar Abdullahi Garba Ramat ya bayyana cewa uwa ga AAZaura hajiya Laure mai kunu ta shaki iskar yanci bayan kokarin da jami’an farin kaya na DSS su kai yi.

Sanann an kubutar da ita ne a jigawa cikin koshin lafiya tare da dawo da ita Kano da hada ta da iyalan ta ba tare an biya kudin fansa ba.
An yi garkuwa da mahaifiyar A.A.Zaura a Hajiya Laure mai kunu a jiya Litinin a gidanta dake Zaura karamar hukumar Ungoggo a Birnin Kano.
Maharan wadanda suka zo gidan a mashin tare da makaman su daga baya su ka bayyana cewa sun isa Katsina da ita.