Wata kotun Majistare da ke zamanta a Jihar Legas ta aike da wani matashi mai suna Mubarak Kajola mai shekara 28 gidan gyaran hali bisa zarginsa da aikata wasu laifuka uku.

Kotun ta aike da matashin ne a ranar Laraba, inda ake zarginsa da satar karafunan da ake rufe mamata da su a wata maƙabarta da ke Jihar.
Kotun ta ce ana kuma zargin matashin da aikata Sata, Keta haddi, da kuma amfani da miyagun kwayoyi.

Jami’a mai gabatar da ƙara Funmi Akinleye ta bayyanawa kotun cewa wanda ake zargi ya shiga makabartar ne ba bisa ka’ida ba tare da keta haddin mamatan da ke kwance a cikin makabartar.

Funmi ta ce matashin ya shiga makabartar ne a ranar Juma’ar da ta gabata, kuma ya sace karafan da kudinsu ya kai naira miliyan daya da dubu dari.
Jami’ar ta kara da cewa a lokacin da matashin ya shiga cikin makabartar a jikinsa akwai wata bindiga.
Wanda hakan ya sanya Alkaliyar kotun ta bayar da umarnin aikewa dashi gidan gyaran hali tare da dage sauraron shari’ar.