Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya rantsar da sabuwar sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.

Magatakardar majalisar, Mista Chinedu Akubueze ne ya gabatar da rantsuwar kama aiki ga Akpoti-Uduaghan yayin zaman majalisa a yau Alhamis.
Bayan yin rantsuwar, Akpabio ya mika wa sabuwar sanatan kwafi na dokokin majalisar ta dattawa.

Daga bisani an mata jagora zuwa wurin zamanta bayan ta gama gaisawa da takwarorinta.

Kotun daukaka kara da ke Abuja, a ranar Litinin, ta jadada nasarar Natasha Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar PDP, a matsayin sanatan Kogi ta Tsakiya.
Kotun daukaka karar ta yi watsi da karar da Sanata Abubakar Ohere ya shigar kan cewa ba ta da inganci.
Tun da farko a watan Satumba, Kotun Sauraron Karar Zaben Jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta soke nasarar Ohere na jam’iyyar APC.
Daga bisani kotun ta ayyana Akpoti-Uduaghan ce ainihin wacce ta yi nasara a zaben sanatan.