Jam’iyyun adawa na PDP da NNPP da sauran wasu jam’iyyu biyar sun dunkule a matsayin jam’iyyar daya a Najeriya.

Sauran jam’iyyun sun hada da SDP, APM, ADC, ZLP, da kuma YPP.

Jam’iyyun sun dunkule a yayin wani taro da suka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyun sun sanyawa jam’iyyar su na da Coalition of Concerned Political Parties CCPP, wato hadakar jam’iyyun siyasa da suka damu da halin da Najeriya ke ciki.

Jam’iyyun sun hade ne tun bayan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga jam’iyyun Adawa wajen kawar da jam’iyyar APC daga kan karagar mulki.

Atiku ya bayyana cewa hadewar jam’iyyun na da muhimmanci domin kare kasar daga komawa tsarin jam’iyya daya.

Hadakar jam’iyyun sun bayyana cewa hadewar za ta karfafa dimukradiyya domin kawo karshen matsalolin da suka addabi Najeriya.

A yayin taron wakilan kowacce jam’iyya sun samu halartar taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: