Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani magidanci mai shekaru 35 da ake zargi ya rataye kansa a Jihar.

Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar DSP Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da Matashiya TV ta wayar tarho a yau Asabar.
Shiisu ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis a kauyen Dungun Tantama da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa ta jihar.

Lawan ya kara da cewa jami’ansu ne suka kwance gawar magidancin daga jikin bishiyar da ya rataye kan nashi tare da kai shi asibiti domin gudanar da bincike.

Shiisu ya bayyana cewa sun samu labarin batan mutumin ne tun a ranar Larabar da ta gabata.
Kakakin ya ce bayan binciken da aka tsananta ne aka gano gawarsa rataye a jikin bishiyar ya mutu.
Sannan su na ci gaba da bincike domin gano dalilin rasuwar mutumin tare da yin bayani ga jama’a a nan gaba.