Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michael Platini ya kammala wa’adinsa na dakatarwa da akayi masa akan harkar kwallon.

An dakatar da Platini ne bayan an kama shi da laifin karya dokar hukumar tare da karbar cin hanci da ya Kai dalar Amurka Miliyan 2 shida Shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Sepp Blatter.
Sai dai har yanzu akwai sauran Rina a kaba kasancewar akwai Binciken da ake masa a kasar faransa akan zargin Rashawa a gasar cin kofin Duniya da zai gudana a kasar Qatar a shekarar 2022.

