Rundunar yan sanda Jihar Gombe ta kama wani matashi mai shekara 18 a duniya mai suna Mustapha Adamu Isah da ake zarginsa da hallaka wata tsohuwa mai shekaru 58.

 

Kakakin rundunar yan sandan Jihar ASP Mahid Mua’zu shi ne ya bayyana haka yayin da yake holen wanda ake zargin a hedkwatar hukumar a ranar Juma’a.

 

Jaridar The Nation ta bayyana cewa jami’an sun kama yaron wanda ake masa lakabi da Abbati ,da ya hallaka matar mai suna Hajiya Aishatu Abdullahi wacce ake kira da Damori a Unguwar Jeka da fari Quarters da ke cikin garin na Gombe.

 

Mai magana da yawun rundunar ya ce a ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba, yan sanda a yankin garin Pantami suka samu labarin faruwar lamarin daga dan matar da aka hallaka.

 

Kakakin ya kara da cewa an kama Abbati ne a ranar 22 ga watan Oktoba da muke ciki, bisa zargin hannu a hallaka matar bayan samun bayanan sirri daga tawagar bincike.

 

Mahid ya bayyana cewa a yayin gudanar da binciken, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga dakin matar ne domin neman sufanarsa da ta kwace masa.

 

Kazalika ya ce wanda ake zargin ya kuma ambaci abokinsa mai suna Idris Abubakar Danjauro mai shekaru 17 wanda ya ce ya je dakin tsohuwar domin ya taya shi aikata ta’addancin.

 

Mahid ya ce bayan kama Idris din ya musanta cewa bai san wanda ya hallaka matar ba.

 

Kakakin ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma da zarar sun kammala bincike za a mika shi gaban kotu domin yi masa hukunci.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: