Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fara gudanar da bincike kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele a ranar Juma’a.

Hukumar na bincikar Emefiele akan bashin dala biliyan 15 da aka ciyo daga ƙasashen waje.


Sannan Emefiele zai kuma yiwa hukumar bayani akan yadda babban bankin ya kashe Naira biliyan 74.84, wajen samarwa da kuma fitar da kudade, ciki har da sabbin takardun kuɗi na Naira da sauran wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.
Zarge-zargen da hukumar ta ke yi masa kari ne akan zargin badakala, wanda jami’in bincike na musamman, Jim Obazee wanda ke duba ayyukan CBN ya bankado.
Obazee wanda kwamitinsa ke hada kai da hukumar binciken yan sandan Najeriya, ya kuma mika rahoton wucin gadi akan CBN ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ya zuwa yanzu kwamitin jami’in EFCC ya fara bincikar Emefiele kan zarge-zarge shida da ake yi masa.