Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa cin zabe ba yawan kuri’un da aka kada ba ne kawai, harda bin ka’idoji.

Doguwa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidan Talabijin na Channels TV yayin da yake mayar da martani kan cece-kucen da ake tafkawa dangane da zaben 2023 a jihar Kano.
Ya ce zabuka a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya a kodayaushe suna kan tsari da ka’idoji, kuma tsayawa zabe bisa wadannan ka’idoji ne ke sa a samu ‘yanci da gaskiya.

Ya ce, a gare shi idan aka tambaye shi abin da ke faruwa a Kano, abin da ya saba faruwa ne, Kano ta kasance jiha ce mai ci gaba, mai fafutuka ta fuskar siyasa da akida.

Sannan ya kara da cewa ya kamata mutane su san cewa bawai a zabi mutum shike nuna yaci zabe ba har sai ya cika dukkan sharudan da za su saka ya zama shugaba ga al’umma.