Rundunar jihar Zamfara ta yi nasrara daƙile wani harin ƴan bindiga tare da kama wata da take kai musu bayanai.

Mai magan da yawun ƴan sandna jihar ASP Yazid Abubakar ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Gusau babban birnin jihar.

Ya ce jami’an su sun samu nasarar daƙile harin bayan shirin ƴan biindiga na kaiwa wani yanki a ƙaramar hukumar Zurmi a jihar.

Ya ce sun yi musayar wuta na tsawon awanni kafin daƙile harin na ƴan bindiga yayin da su ka kai musu hari ofishinsu da ke Zurmi a jihar.

A sakamakon haka sun samu nasarar kama guda daga ciki yayin da sauran su ka tsere ɗauke da raunin haribin bindiga a jikinsu.

Ƴan sandan sun kama wata mace mai shekaru 35 mazauniyar garin Rukudawa da ake zargi da kaiwa yan bindiga bayanai kuma tuni su ka ffara bincike a kanta.

Kakakin yan sandan jihar ya ce matar ta bayyana musu cewar ta kasance ta na aiki ne da ƴan bindigan ƙarƙashin jagoransu Ɗanƙarami.

Ƴan sandan sun kwato bindigu ƙirar AK47 guda biyu tare da babur, wayoyin hannu da harsashi kuma su na ci gaba da bibiyar don kama waɗanda su ka tsere.

Sannan a ranar 27 ga watan Yuli da ya gabata ƴan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi ƴan bindiga ne a yankin Saminaka da ke ƙwaryar binin Gusau babban birnin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: