Yanzu Malamai Sun Koma Gogayya Da Ƴan Siyasa Wajen Neman Iko – Sule Lamido
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana damuwarsa game da yawan kutsen malamai cikin harkokin siyasa, inda ya ce yanzu malamai su na matuƙar kwaɗayin samun iko akan…
Gwamnatin Jihar Neja Za Ta Karya Farashin Kayan Abinci Ga Al’ummar Jihar Sakamakon Gabatowar Azumin Watan Ramadan
Gwamnatin jihar Neja ta sanar da ƙudurinta na raba manyan motocin kayan abinci guda 1,000 akan farashi mai sauƙi a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 25, a matsayin tallafi ga al’ummar…
Matasa Kadara Ce Ga Nahiyar Afirka Ba Nauyi Ba – Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya buƙaci shugabannin yankin nahiyar Afirka, da su ɗauki matasan yankin a matsayin kadara da za a iya dogaro da ita a fannoni…
Kamfanin Mai Na Ƙasa NNPCL Ya Musanta Iƙirarin Rashin Ingancin Man Da Ya Ke Samarwa
Kamfanin samar da man fetur na ƙasa NNPCL ya musanta wani iƙirari cikin wani hoto mai motsi da ya karaɗe shafukan sada zumunta, akan rashin ingancin man da su ke…
Gwamnatin Najeriya Za Ta Sake Ciyo Bashin Dala Miliyan 300 Daga Bankin Duniya
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci bankin duniya da ya bata sabon bashin Dala miliyan 300, dan bunƙasa ɓangaren kula da harkar lafiya a Najeriya. Sanarwar da aka samo daga bankin na…
Sanata Shehu Sani Tare Da Wasu Jiga-Jigai Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC A Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya karɓi Sanata Uba Sani tare da wasu jiga-jigan ƴan siyasa a jihar, zuwa jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC. Uba Sani ya kuma tabbatarwa…
Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Hudu A Jihar
Rundunar yan sandan Najeriya ta hallaka wasu mutane hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi da kuma kwato…
Mutane 23 Sun Mutu Wasu Sun Jikkata A Hadarin Mota A Kano
Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta ƙasa FRSC ta bayyana cewa, mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani haɗarin mota da ya afku ranar Alhamis, a gadar sama ta Muhammadu…
Gobara Ta Lalata Kayayyakin Hukumar Zabe A Sokoto
Hukumar zabe Mai zaman Kanta ta Kasa INEC ta Jihar Sokoto ta tabbatar da konewar ofishinta da ke cikin Ƙaramar hukumar Gwadabawa a Jihar, bayan tashin gobara a Ofishin. Kwamishinan…
Ya Zama Wajibi Kasar Canada Ta Fito Ta Fadi Dalilin Hana Manyan Sojin Najeriya Shiga Kasarta – Matawalle
Karamin Ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnatin Tarayya ta dauki mataki mai karfi akan kasar Canada bisa hana hafson tsaron Kasar nan Janar Christopher…
